fidelitybank

A gudanar da addu’o’i a Masallatai domin samun sauƙin rayuwa a Najeriya – MURIC

Date:

Ƙungiyar kare hakkin bil’Adama ta Musulunci a ƙasar nan (MURIC), ta buƙaci a gudanar da addu’o’i a masallatai da coci-coci a ƙasar kan abubuwan da ta kira da munanan alamu a harkokin siyasar Najeriya.

Babban Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya gabatar da buƙatar a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.

Ƙungiyar ta nuna cewa yin adduo’i a masallatai da majami’u bukata ce da ta zama dole bisa la’akari da yadda baƙin al’amuran ke neman zama barazana ga makomar kasar baki ɗaya.

Saboda haka MURIC ta yi kira ga dukkan limaman Musulmi da su jagoranci mabiya a masallatansu a gobe Juma’a 9 ga watan Agusta, su yi addu’o’in, kamar yadda su ma limaman Kiristoci, su jagoranci mabiyansu wajen yin addu’ar a ranar Lahadi mai zuwa, 11 ga Agustan.

Farfesa Akintola ya ce waɗannan abubuwa na tashin hankali da suka lullube matasa a duniya, munanan alamomi ne da suke matuƙar buƙatar yi wa Najeriya addu’o’i.

Shugaban ya kuma ce su ma masu mulki akwai buƙatar yi musu addu’a ta samun kariya da kuma sanya tausayin talakawa wajen gudanar da mulkinsu.

Ƙungiyar ta MURIC, ta yi kiran ne sakamakon zanga-zangar lumana da ta rikiɗe ta zama tarzoma -ta kashe-kashe da lalata dukiyar al’umma wanda ta ce, ƙasar na cikin mawuyacin hali.

Baya ga wahalhalun da ke tattare da durƙushewar tattalin arziƙi, zanga-zangar matsin rayuwa na ci gaba da fito da wasu al’amura marasa daɗi, ga ƙasar in ji ƙungiyar ta MURIC.

Sanarwar ta kara da cewa hatta masu shirya zanga-zangar ba su yi tsammanin irin wannan mummunan lamari zai faru ba.

yola news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...
X whatsapp