Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayar da umarnin tashin masu hada-hadar da ke kan hanyar da ta ratsa yankunan Mabushi, Jahi da Kado.
Wike ya bayar da wannan umarni ne a Abuja ranar Talata lokacin da ya ziyarci yankin da aka fi sani da ‘Road N12’ a gundumar Mabushi da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana yankin, wanda ke bayan Unguwar Minista a gundumar Mabushi, a matsayin “barazana” ga tsaron birnin.
Yan fashin da aka fi sani da ‘Baban Bola’ sun mamaye yankin da suka hada da kanikanci da masu kera kayan daki.
Ministan wanda ya samu rakiyar tawagar jami’an tsaro da kuma manyan jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja, ya kara da cewa za a kara kaimi wajen ganin an kawar da masu aikata laifuka a birnin.
Wike ya ce ba za a bar irin wadannan gungun masu aikata laifuka a cikin FCT ba.
Ya ce yankin ya kuma samu kwarin gwiwa saboda kaurin itatuwan cashew da ’yan asalin babban birnin tarayya suka dasa don hasashe.
Wike ya yi gargadi game da dasa irin wadannan bishiyoyi a wuraren da gwamnati ta tsara don ci gaba.
A cewarsa, gwamnati ba za ta biya diyya ga itatuwan ba.
Wike ya umurci Sashen Kula da Raya Kasa da Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya da su share yankin gaba daya tare da daukar iyakacin hanyar domin gudanar da ayyukan farko.
“Kada ku biya su diyya. Wannan maboyar miyagu ce, don haka ya kamata al’umma su daina dasa itatuwa a yankin.
“Lokacin da suka ga gwamnati na da niyyar bunkasa hanyar sai su zo su shuka amfanin gona domin gwamnati ta biya diyya. Ba za mu yi wani diyya ba.
“Dole ne hukumar raya kasa ta share wannan yanki, ta kori duk wadannan masu aikata laifuka.
“Waɗannan abubuwa ne da kuke gani mutane suna aikata laifuka sannan kafin ku sani sai su ruga a nan don fakewa, mutane za su ce oh, FCT ba lafiya.
“Ba batun ba su sanarwa ba ne. Babu sanarwa. Dole ne ku fatattake su yanzu kuma ku share yankin gaba daya,” in ji shi.