Kungiyar matan gwamnonin kasar nan sun bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su ayyana dokar ta-baci a kan bangaren shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar su da nufin hada karfi da karfe domin shawo kan matsalar.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a ranar Talatar nan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar kuma uwargidan gwamnan jihar Kwara, Ambasada Olufolake Abdulrasaq.
Wannan ci gaban ya biyo bayan kammala wani horon kwanaki biyu da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta shirya wa matan gwamnonin a Abuja.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA Femi Babafemi ya fitar a ranar Talata, ta ce, matan gwamnonin sun amince da bukatar gaggawar karbe iko tare da sake karfafa kwamitocin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi domin gudanar da ingantattun ayyuka jihohin kasar nan.
Sun jaddada bukatar Gwamnatin Tarayya da Gwamnonin Jihohi da su ayyana dokar ta-baci a kan amfani da miyagun kwayoyi da kuma fataucin miyagun kwayoyi da nufin samar da kayan aiki domin tunkarar kalubalen.