Kotun Ecowas ta umarci sojojin Nijar da su gaggauta sakin Mohammed Bazoum da suka tsare tun daga ranar 26 ga watan Yuli da suka hamɓarar da shi.
Kotun ta nemi a gaggauta sakin sa ba tare da wani sharaɗi ba sannan a mayar da Bazoum kan kujerarsa, kamar yadda alƙalin kotun ya faɗa a ƙarar da aka saurara a Abuja, babban birnin Najeriya.
A ranar Alhamis ne ƙungiyar ta Ecowas ta sanar da cikakkiyar dakatarwar da ta yi wa Nijar sanadiyyar juyin mulkin.
A baya, wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar sun yi watsi da hukuncin kotun ta Ecowas.
“Mohamed Bazoum ne yake wakiltar Nijar … kuma har yanzu shi ne shugaban Jamhuriyar,” kamar yadda hukuncin kotun ya bayyana.
“Akwai haƙƙoƙin da aka take.” An tsare Bazoum a gidansa na shugaban ƙasa tare da mai ɗakinsa da ɗansu tun lokacin da aka tsige shi.
A tsakiyar watan Satumba ne, hamɓararren shugaban ya nemi kotun ta Ecowas ta bayar da umarnin sakin shi tare da mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya.