fidelitybank

A gaggauta kuɓutar da mutanen da harin jirgin ƙasa na Kaduna ya rutsa dasu – Buhari

Date:

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa jirgin kasa da ke ɗauke da fasinja kusan 1000 a hanyar Abuja zuwa Kaduna, yana mai bayyana al’amarin a matsayin wani abin damuwa matuka.

A cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Buhari ya ce, kamar sauran ‘yan Najeriya, ina cikin jimami matuƙa da faruwar wannan lamarin, wanda shi ne irinsa na biyu, wanda ya kai ga sanadin mutuwar fasinjojin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba da kuma wasu da suka samu raunuka.

“Harin da aka kai kan jirgin kasa, abin takaici ne; tunani na yana kan iyalan waɗanda suka rasu da kuma addu’a ga wadanda suka jikkata,” in ji Buhari.

Shugaban ya ce, ya bayar da umarnin gaggawa na tabbatar da bincike da hanyoyin magance matsalar tsaron titin jigin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

Sannan ya umarci jami’an tsaro su kuɓutar da fasinjojin da daka sace tare da farautar ƴan bindigar.

Bayanai sun nuna cewa, kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin, wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.

Rahotanni sun ce an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da ‘yan uwan fasinjojin da ke cikin jirgin.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp