Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakanin ƙasar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda ya shafi jigilar jirage da bayar da biza takanin ƙasashen biyu.
Tinubu ya yi kiran ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan UAE a Najeriya Ambassador, Salem Saeed Al-Shamsi a fadarsa da ke Abuja.
A shekarar da ta gabata ne UAE ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriya bayan da kamfanin jirgin sama na Emirates ya dakatar da jigila a Najeriya saboda hana shi wasu haƙƙoƙinsa, saboda wasu ƙa’idoji na kuɗaɗen ƙasashen waje.
Kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne bayan duk wani yunƙuri da ya yi na warware matsalar da hukumomin Najeriya ta hanyar lalama ya ci tura.
Shugaba Tinubu ya ce ya kamata a gaggauta warware matsalar, yana mai cewa a shirye yake ya shiga tsakani da kansa, don kawo ƙarshen matsalar.
“Mu kalli abin a matsayin saɓani na ‘yan uwataka, domin mu warware shi cikin sauki, dole mu yi aiki tare, Muna buƙatar amincewa da dokokin bai daya kan jigilar jiragen sama da batun ‘yan ci-rani,” in ji Tinubu


