Uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta roƙi a haɗa karfi da karfe don ganin kurar rikicin Sudan ta kwanta.
Jaridar Premium Times ta ruwaito, Aisha Buhari na wannan kira a wani taro da ta jagoranta jiya Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewar jaridar, Aisha Buhari na ganin akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji Sudan.
Tun ranar 15 ga watan Afrilu, yaƙi ya ɓarke a Sudan kuma har wannan lokaci, an kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.
Sama da mutane 500 ake kyautata zaton cewa rikicin ya yi sanadin sun rasuwarsu kawo yanzu