Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato a ranar Asabar ya ba da umarnin rufe makarantar Saint Academy da ke Busa Buji a karamar hukumar Jos ta Arewa cikin gaggawa.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin kame masu sana’ar hakar ma’adinai a kewayen mazauna jihar.
A ranar Juma’a ne wani bene mai hawa biyu ya ruguje a makarantar, inda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20 da suka hada da dalibai da malamai, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Alfred Alabo, ta tabbatar da mutuwar mutane 22 tare da ceto wasu 132, daga cikinsu suna samun kulawa a wasu manyan cibiyoyin lafiya a babban birnin jihar.
Mutfwang ya bada umarnin ne a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.
“Ina ba da umarnin rufe makarantar Saint Academy da gaggawa.
“Kuma ina kuma umarci jami’an tsaro da su kama duk wani mai aikin hako ma’adinai a yankunan da ke fadin jihar.”
Da yake jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta dauki nauyin kula da wadanda suka jikkata.


