Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su.
Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman, Ajuri Ngelale, ya fitar yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-haren da ake kaiwa a fadin ƙasar nan.
A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-haren, shugaban ya jaddada cewa, za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma tarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya da sauran masu tayar da zaune tsaye a kowane ɓangaren ƙasar nan.
Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’ar A… ya jikan waɗanda suka rasu.