Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan harin da aka kai ranar Lahadi kan wata motar safa da ke jigilar ‘yan jarida a cikin ayarin motocin tsohon gwamnan Legas, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu.
Lamarin ya faru ne tsakanin Ebute-Ero da Adeniji, Iga-Iduganran, a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ziyarci fadar Oba na Legas, Oba Rilwan Akiolu.
Gwamna Sanwo-Olu ya kuma ba da umarnin cewa dole ne a kamo wadanda ke da hannu a lamarin tare da hukunta su. Bayan haka. gwamnati za ta karbi kudin asibiti na wadanda suka jikkata a lamarin.
Ya ce: “Gwamnatin jihar Legas ta yi Allah wadai da lamarin. Muna mutunta kafafen yada labarai kuma gwamnati a kodayaushe tana tabbatar da cewa sun samar da yanayi mai kyau don gudanar da ayyukansu.”
“Ba za a bar kowa ko kungiya su lalata dangantakarmu da kafafen yada labarai ba. Legas ba ta da wurin ’yan iska.”
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka tarbi Tinubu cikin jerin gwano da murna daga magoya bayansa.