fidelitybank

A gaggauta bincike a kan wanda suka jefa Bam ga masu Maulidi – Gwamnan Kaduna

Date:

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna matukar damuwarsa, kuma ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar, a yayin wani hari na jirgi maras matuƙi mallakar sojojin Najeriya.

Lamarin da ya faru a lokacin da “sojin na Najeriya suka yi yunƙurin kai farmaki kan ƴan bindiga,” kamar yadda sojojin suka tabbatar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata sanarwar da ya fitar a yau, Litinin.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da wasu mutane suka taru domin gudanar da bikin Mauludi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane “bisa kuskure” tare da jikkata wasu da dama.

“Gwamnatin jihar ta aike da manyan jami’anta don tantance halin da ake ciki, da bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma ba da shawara kan daukar matakan gaggawa don rage musu radadi.

“Ina tabbatar wa ƴan jihata cewa har yanzu kariyarsu ce abin da muka fi bai wa fifiko a yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi da masu aikata laifuka a jihar.” in ji sanarwar

Wadanda suka samu raunukan za su samu kulawar gaggawa a asibitin koyarwa na Barau Dikko, inda gwamnati ta dauki nauyin kula da lafiyarsu.

Haka nan gwamna Sani ya yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da marawa jami’an tsaro da gwamnatin jihar baya a yakin da suke yi da masu aikata laifuka.

leadership newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp