Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul’aziz, ya bai wa masallatan ƙasar umarnin gabatar da sallar roƙon ruwa a ranar Alhamis mai zuwa.
Shafin Facebook da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Makkah da Madina na ne ya sanar da hakan a yau Litinin.
Sarki Salman ya ce cikin masallatan da za a yi sallar roƙon ruwan har da na Ka’aba da na Manzon Allah da ke Madina. In ji BBC Hausa.