Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta ce za ta iya komawa yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon rashin cika alkawarin gwamnatin tarayya.
Shugabannin ASUU na rassa su na zargin gwamnatin Buhari da watsi da yarjejeniyar da a ka cin ma, a karshen makon nan za a kira taron NEC inda ASUU za ta dauki mataki a kan batun yajin aikin.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, ASUU ta reshen jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola da ke garin Ogbomoso, a ihar Osun ta na zargin gwamnatin da rashin cika alkawura.
Shugaban ASUU da sakatarensa na jami’ar, Dr. Biodun Olaniran da Dr. Toyin Abegunrin, sun fitar da jawabi bayan babban taron da aka yi na ranar Litinin da ta wuce.