Kotun Ƙolin Saudiyya ta nemi ‘yan ƙasar su fara duba jaririn watan watan Ramadana daga yammacin ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu.
Hakan ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban na shekarar Hijira ta 1446 a kalandar Musulunci.
Shafin Inside the Haramain ya ruwaito cewa an umarci duk wanda ya ga watan ya kai rahoto ga reshen kotun mafi kusa da shi.
A Najeriya ma za a fara duba watan ne daga Juma’a, saboda ya yi daidai da ranar ƙarshe ta watan na Sha’aban.
Ganin sabon watan na nufin Musulmai za su fara ibadar Azumin Ramadana mai girma, inda za su shafe kwana 29 ko 30 suna guje wa ci ko shan wani abu tun kafin fitowar rana har zuwa faɗuwarta.