Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya bukaci al’ummar Musulmi su soma laluben sabon watan Dhul-Hijjah daga gobe Laraba.
Sultan Abubakar ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya fitar, yana cewa Laraba ita ce 29 ga watan Dhul-Qidah 1443AH, kuma ita ce ranar soma duba sabon wata na Dhul-Hijjah 1443AH.
Ya kuma roki Allah ya taimakawa al’ummar Musulmi wajen tafiyar da harkokin ibada a cikin sabuwar watan mai alfarma.
Dhul-Hijjah shi ne wata na 12 kuma na Æ™arshe a kalandar Musulunci da al’ummar Musulmi ke gudanar da Hajji da kuma bikin Sallah Babban – da gudanar da layya.