fidelitybank

A fara duban jinjirin Watan Sahhawal ranar Alhamis – Sarkin Musulmi

Date:

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta ƙasa, Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi da su duba jinjirin watan Shawwal na shekarar 1444 bayan hijira daga ranar Alhamis.

Abubakar ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi.

“Ana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu, daidai da 29 ga watan Ramadan 1444, ita ce ranar neman jinjirin watan Shawwal 1444.

“Saboda haka an bukaci musulmi da su fara neman jinjirin watan Shawwal na shekara ta 1444 a ranar Alhamis, kuma su kai rahoto ga Hakimin Kauye mafi kusa da su domin su samu damar tattaunawa da Sarkin Musulmi,” in ji Junaidu.

Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah ya taimaki Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa ganin jinjirin wata zai nuna cewa an kawo karshen azumin farilla na wata guda da musulmi ke yi a fadin Najeriya.

Shawwal shine wata na 10 a musulunci.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp