Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce iyalan Muhammadu Buhari sun yanke shawarar yi masa jana’iza a garin Daura mahaifarsa da ke jihar ta Katsina.
Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta DW Hausa, Dikko Radda ya ce yana birnin na Landan ya samu labarin rasuwar inda ya je duba shi.
“Na zo ranar Juma’a domin duba shi, muna shirin dawowa gida kuma sai ga labarin rasuwar tasa,” in ji shi.
“Yanzu muka rabu da iyalansa a asibitin da ya rasu kuma an yi ittifaƙi za a kai shi gida Daura a jihar Katsina domin yi masa sutura. Insha Allau za su baro Ingila da safe.
“Muna sa ran gobe Litinin za a yi jana’izar tasa saboda muna sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai iso Ingila cikin dare, su taho da mamaci da safe.”
Fadar shugaban Najeriya ta ce Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya je Landan domin raka gawar Buhari zuwa gida Najeriya.