fidelitybank

A dakatar da fadar sakamakon zabe – Atiku

Date:

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, ya yi fatali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya da ake ci gaba da fitarwa, inda ya yi kira da a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar wanda ya samu sa hannun mai magana da yawun ta dakta Daniel Bwala, ta ce hukumar zaɓe ta dakatar da karɓa da kuma sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ta ke yi.

Daniel Bwala ya ce dakatar da karɓar sakamakon ya zama tilas don shawo kan matsaloli da jam’iyyu suka yi korafi a kai dangane da rashin amfani da na’urar BVAS da kuma kasa tura sakamakon zaɓen zuwa shafin INEC.

Sanarwar ta ce abin da ya kamata INEC ta yi a yanzu shi ne sanya sabon ranar gudanar da zaɓe a wuraren da aka fuskanci matsalar, tare da tabbatar da cewa an aika sakamakon zuwa shafin yanar gizo na hukumar zaɓe.

Sanarwar kwamitin ya ƙara da cewa a soke dukkan sakamakon zaɓen da aka sanar har sai lokacin da aka aika sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe zuwa shafin INEC.

Kwamitin ya kuma ce INEC ta fito ta yi wa ‘yan ƙasa jawabi kan sahihancin zaɓe da ta gudanar don samun ƙwarin gwiwa daga ‘yan ƙasar da ma al’ummomin ƙasashen waje.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp