Karamin Ministan Ilimi, Yusuf Sununu, ya yi kira da a daina nuna wariya ga yara masu nakasa a makarantun gwamnati a fadin kasar nan.
Sununu ya yi wannan bukata ne a wajen taron tunawa da ranar nakasassu ta duniya ta 2023 da aka gudanar a Abuja.
Ministan wanda Dr Clarence Ujam na ma’aikatar ilimi ya wakilta, ya ce binciken ya nuna cewa ana kin yara masu nakasa a makarantun gwamnati saboda rashin kayan aiki da masu kula da su, lamarin da ya ke son duk masu ruwa da tsaki su hada hannu su daina.
“Bincike ya nuna cewa yara masu nakasa ana watsi da su daga makarantun gwamnati saboda rashin kayan aiki da masu kula da su. Dole ne a dakatar da wannan nuna wariya ta hanyar hadin gwiwa na dukkan masu ruwa da tsaki,” inji shi.
Ya ce kuma abin takaici ne yadda yara masu nakasa, baya ga ilimi, ana tauye musu hakkinsu da dama, ciki har da munanan hasashe.
Don haka ya yi kira da a aiwatar da kudurin ci gaba mai dorewa mai lamba 4, wanda ke bukatar hada kai da bunkasa damammaki ga nakasassu.


