Gwamnatin tarayya ta ce, ta rufe shagunan sayar da magunguna 358 a babban birnin tarayya Abuja cikin kwanaki hudu.
Ta bayyana cewa, rufe wuraren harhada magunguna da laifuffuka daban-daban da suka hada da yin aiki ba tare da rajista ba, lasisin jabu, rarraba kayan aikin da’a ba tare da sa ido kan magunguna ba, rashin ajiya da tsaftar muhalli da dai sauransu ya yi daidai da manufarta na tabbatar da cewa, magungunan da ‘yan Najeriya ke amfani da su.
Magatakardar Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN), Pharm Ibrahim Ahmed, wanda ya bayyana haka a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa, an kama wasu masu sayar da magunguna guda hudu, kuma suna fuskantar shari’a.