Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya dage cewa, ya kamata a bar yankin Kudu maso Gabas su samar da shugaban Najeriya a 2023.
Da yake magana a lokacin da yake jawabi ga mambobin kwamitin harkokin siyasa (PAC) na Ohanaeze Ndigbo a Abeokuta, Obasanjo ya bayar da hujjar cewa shugabancin Kudu-maso-Gabas zai tabbatar da zaman lafiya, adalci da ci gaban kasa a kasar.
Mambobin kwamitin sun ziyarci tsohon shugaban kasar ne a dakin karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo domin neman goyon bayan sa kan neman shugabancin yankin Kudu maso Gabas a 2023.
Obasanjo ya yi gargadin cewa “rashin fahimta ba zai iya haifar da kyakkyawan tsarin gina kasa da ci gabanmu ba.”