fidelitybank

A baiwa Likitoci damar shiga Gaza – Ƙungiyar Agaji ta Duniya

Date:

Kungiyar Bayar da Agaji ta Duniya ta Red Cros (ICRC), ta ce yayin da aka shigar da kayan agajin da ake buƙata zuwa Gaza, ankwai buƙatar shigar da likitoci domin rage ƙarancin jami’an lafiya da asibitocin yankin ke fuskanta.

“Babban abin da ake buƙata a yanzu shi ne ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Gaza,” kamar yadda Sarah Davies ta ICRC ta shaida wa BBC.

Ta ƙara da cewa ba kayan agajin kaɗai ake buƙata ba, “har da jami’an lafiya da tawagar likitoci waɗanda za su rage wahalhalun da ake fuskanta a asibitocin yankin”.

A jiya ne aka buɗe mashigar Rafah da ke kan iyakar Masar da Gaza domin bayar da dama ga manyan motoci 20 maƙare da kayan agaji suka shiga Gaza, ƙarƙashin wata yarjejeniyar da aka cimma da Isra’ila.

To amma Misis Davies ta ce akwai buƙatar ci gaba da shigar da kayan agajin.

“Akwai buƙatar ci gaba da shigar da agajin, mota 20 ba za ta wadaci mutanen da ke buƙatar tallafi ba, haƙiƙa ana cikin wani mawuyacin hali,” In ji ta.

“Muna yawan zantawa da tawagarmu da ke wurin, kuma yadda suke bayyana mana yanayin wurin yana da matuƙar tayar da hankali.”

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp