Yan bindiga sun hallaka wani Basaraken gargajiya a jihar Filato, yayin da yake kan hanyar zuwa gaishe damara lafiya a Asibiti.
Wani mazaunin yankin ya ce, tuni aka ɗakko gawarsa aka mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Maharan waɗan da ake zaton yan fashi da makami ne, sun farmaki Sarakuna biyu, ɗayan ya koma gida.
Daily Trust ta rawaito cewa, maharan sun kashe ɗaya daga cikin su mai suna, Mustafa Ibrahim, wanda ke rike da sarautar Garkuwan Yala.
Lamarin ya faru ne kwana ɗaya, bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Pinau a wannan yankin, inda suka yi gaba da ɗaruruwan dabbobi, kuma suka ƙona gidaje da kayan abinci.