Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla ‘yan Najeriya 24,000 ne suka ɓata tun daga shekarar 2014 waɗanda galibinsu yara ne ƙanana, sanadiyyar rikicin Boko Haram.
Kakakin ƙungiyar Aliyu Dawobe ya shaida wa BBC cewa jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne kan kan gaba inda suke da adadiu 16,000.
Aliyu Dawobe ya ce ƙungiyarsu ta samu ƙorafe-ƙorafe daga mutane daban-daban da ƴan’uwansu suka ɓata, kuma tana bakin ƙokarinta wajen taimaka musu domin gano yaran.
ICRC ta ce ko a wannan shekarar kadai ta gano mutum 11 ƙari kan mutane 13 da aka gano a 14.
Kakakin ƙungiyar ya ce wasu daga cikin ririn waɗannan mutane sun watsu ne cikin duniya, yayin da wasunsu ke tsare a hannun hukumomi, wasu kuma sun sake garuruwa.