Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele na fuskantar karin tuhume-tuhume 14, yayin da masu shigar da kara a Najeriya ke kara tsananta shari’ar da aka fara a watan Yunin da ya gabata bayan rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu.
Lamarin ya sa an dakatar da Emefiele tare da korarsa daga aiki watanni hudu da suka gabata.
A watan Nuwamba ne dai Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara tuhumar Emefiele da laifuka shida da suka haɗa da zamba da suka kai Naira biliyan 1.2.
Yayin da aka ci gaba da shari’ar a babbar kotu birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, ya ce an gyara tuhume-tuhumen da suka hada da na jabu, da laifin karya amana, samu ta hanyar karya da kuma bayar da cin hanci da rashawa.
Sabbin tuhume-tuhumen na zuwa ne bayan rahoton da wata tawagar shugaban kasa ta kafa domin gudanar da bincike a kan zargin aikata ba daidai ba a babban bankin kasar.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya bukaci lokaci domin duba sabbin tuhume-tuhumen kafin shigar da kara.
Duk da cewa an bayar da belinsa a watan Disamba, tare da takaita zirga-zirgarsa a babban birnin kasar, Abuja kaɗai.
Amma, a zaman da aka yi na ranar Alhamis, an gyara wadannan takunkumin, kuma a yanzu yana iya tafiya ko’ina cikin kasar.


