Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane 9, sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano.
An kuma bayyana cewa wadanda suka jikkata mutane 10 ne.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da kodinetan hukumar NEMA na yankin Kano, Dakta Nuradeen Abdullahi, ya fitar a yammacin ranar Talata.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su guji yada labaran karya.