Jose Peseiro ya sake jaddada burinsa na jagorantar Super Eagles, don samun daukaka a gasar cin kofin Afrika ta 2023.
Najeriya wadda ta lashe sau uku, za ta yi kokarin lashe kofin karo na hudu a Cote d’Ivoire.
Super Eagles za ta fafata ne da mai masaukin baki wato Guinea-Bissau da Equatorial Guinea a rukunin A.
Kasashen yammacin Afirka sun dandana kudarsu a nahiyar a shekarar 2013.
Peseiro duk da haka yana da karfin gwiwar kungiyarsa na iya sake zama mafi kyawun kungiya a nahiyar.
“Kwarewa na da ‘yan wasan Najeriya na da kyau sosai. Kasancewa cikin wasan kwallon kafa na Afirka da Najeriya abu ne mai ban sha’awa, kuma ba zan iya musun hakan ba,” in ji Peseiro kamar yadda KORAPLUS ya ruwaito.
“Na gaya wa kowa cewa ina so in lashe gasar cin kofin Afrika tun farkon lokacin da na rattaba hannu kan kwantiragin da ‘yan wasan Najeriya, kuma muna nazarin abokan hamayyar mu da kyau domin samun nasara, kuma wannan shi ne abin da muke neman cimma.”
Super Eagles za su fara shirye-shiryen tunkarar gasar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa mako mai zuwa ranar Talata.


