Malam Aminu Ringim, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jam’iyyar PDP a Jigawa, ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar.
Ringim ya yi takarar gwamna sau biyu a 2015 da 2019 a tsarin jam’iyyar PDP amma ya kasa lashe zaben.
Alhaji Musa Abubakar, jami’i mai kula da zaben fidda gwani na jam’iyyar NNPP a jihar Jigawa, ya bayyana Ringim a matsayin wanda ya lashe zaben, jim kadan bayan kammala ka’idojin da suka dace a ranar Litinin da ta gabata a Dutse.