Rotimi Amaechi, dan takarar shugabancin kasa a jamâiyyar All Progressives Congress (APC), ya ce, yaki da rashin tsaro a Najeriya shi ne babban abin da ya sa a gaba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Amaechi ya yi wannan alkawarin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, bayan ziyarar da ya kai majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Bayelsa a Yenagoa a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da ya ke tattaunawa a fadin kasar nan kan muradun sa na shugaban kasa.
Amaechi, wanda ya kuma gana da wakilan jamâiyyar a Bayelsa domin neman goyon bayansu a zaben fidda gwani na shugaban kasa mai zuwa, ya ce maganin miyagun laifuka shi ne a baiwa mutane alhaki tare da sanya su samun hanyoyin samun kudaden shiga.