Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira miliyan 18 ga iyalan mutane tara da aka kashe a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa hari.
Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna KADSEMA, Muhammed Mukaddas ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kaduna.
Ya ce, a ranar 19 ga watan Afrilu ne gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya amince da bayar da Naira miliyan 2 kowanne ga iyalan wadanda suka mutu a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna. A cewar Daily Nigerian.