Gwamnatin jihar Kano ta ce zta mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma, game da illar dumamar yanayi da gurbacewar muhalli a shekarar 2022.
Kwamishinan muhalli na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, bayan kammala duba tsaftar muhalli da aka gudanar na Asabar din karshen wata a Kano.
Kwamishinan ya ce, “Za mu yaki zubar da shara barkatai da wuraren da ba su dace ba, wanda hakan yakan gurbatar da iska, ta janyo dumamar yanayi waddake baraza ga rayuwar tsirrai”.
“Akwai bukatar alumma su kasance masu bin doka ta tsaftar muhalli da ma dukkan sauran dokokin da ake sanyawa a kowanne lokaci, wanda hakan zai taimaka wajen kawo ci gaban jihar Kano da ma kasa baki daya”. In ji Dr. Kabiru.