fidelitybank

HISBA ta kamo masu siyar da Shisha a Kano

Date:

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kai sumame shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama masu shagunan dake siyar da Shisha.

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnati ta fara aiwatar da dokar a faɗin jihar, tun bayan da majalisar dokoki ta sanyawa ƙudurin dokar hannu akan sha da siyar da Shisha.

Sashi na 13(7) na dokar sisha, wacce a ka sanyawa hannu a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021, ya ce sha da ta’ammali da shisha haramun ne a Jihar Kano.

Tuni dai hukumar ta fara kama masu sayar da shisha a jihar, inda su ma su ka ce duk da an hana, har yanzu ana kawo musu ita da ga kasashen Dubai da China.

Haka kuma sun yi ƙorafin cewa an fara aiwatar da dokar ne ba tare da an basu wa’adi ba.

Sun kuma ƙara da cewa ya kamata a ce an wayar musu da kai da kuma sanarwa mai tsawo kafin a zo a fara kai musu farmaki a wajajen sana’ar su.

Sun ce su sun za ci dokar ta tsaya ne a wajen masu guraren shan shishar ba wai dillalin ta ba.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Shugaban Hukumar Hisbah, Muhammad Harun Ibn-Sina, ya ce, sun fara sumamen ne domin haka ayyukan hukumar ya gada.

A cewar sa, sashe na 13(7) na dokar hana shisha ya tabbatar da cewa ta an haramta amfani da ita a jihar Kano, inda ya jadda ƙudurin hukumar Hisbah na ci gaba da hana sha da sayar da ita a faɗin jihar.

A ƙarshe ya kuma jaddada ƙudurin hukumar wajen yaƙi da baɗala da kuma umarni da kyawawan ayyuka a jihar.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp