Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Litinin ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Osinbajo ya ziyarci jihar Ogun ne domin wata tattaunawa da kungiyar hadin kan Afrika ta shirya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tattaunawar mai taken, ‘West Africa: Rising to the Challenge of Consolidating Democracy Governance’ an shirya gudanar da shi ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo, dake Abeokuta, a ranakun Litinin da Talata.
Osinbajo ya sauka a harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo da misalin karfe 10:24 na safe.
Osinbajo, wanda ya samu rakiyar gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da sauran su, daga bisani Obasanjo ya tarbe su yayin da suka wuce wurin da aka shirya taron.