fidelitybank

2023: Manyan ‘yan siyasa da za su iya zama shugaban kasa – Malmain Majami’a

Date:

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, a ranar Litinin ya bayyana wasu manyan ‘yan siyasa da a ke ganin za su iya zama shugaban kasa da mataimakinsa a Najeriya a 2023.

Primate Ayodele ya bayyana sunayen gwamnonin kamar haka, Aminu Tambuwal, Nyesom Wike, Samuel Ortom, Mohammed Bala, Emmanuel Udom, Seyi Makinde, da Ifeanyi Ugwuanyi a matsayin nagartattun ‘yan takarar shugaban kasa a bangaren jam’iyyar PDP.

Ya kuma bayyana Bukola Saraki, da Peter Obi a matsayin wadanda za su iya tsayawa takara.

Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele, ya sanya wa hannu, ya ambaci Abubakar Malami da Boss Mustapha da Kayode Fayemi da Rotimi Amaechi da Farfesa Babagana Zulum da Babatunde Raji Fashola sai Mai Mala Buni da Ibikunle Amosun da Godswill Akpabio, da kuma Rauf Aregbesola a matsayin wanda za su iya tsaya takara a matsayi shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa mutane da yawa za su fafata da kansu a manyan jam’iyyun siyasa biyu kuma akwai bukatar su kasance masu dabara a siyasa.

A cewar Primate Ayodele: “Wasu ‘yan siyasa an nada su ne, domin su zama shugaban kasa da mataimakin shugaban Najeriya kuma idan jam’iyyunsu su ka ba su tikitin.

“A PDP, ya ambaci Aminu Tambuwal da Nyesom Wike da Bukola Saraki da Samuel Ortom da Bala Mohammed da Emmanuel Udom tare da Seyi Makinde da kuma Ifeanyi Ugwuanyi da Peter Obi.

“A APC, akwai Abubakar Malami da Boss Mustapha da Kayode Fayemi da Rotimi Amaechi da Farfesa Babagana Zulum da Babatunde Raji Fashola sai Mai Mala Buni da Ibikunle Amosun da Godswill Akpabio da Rauf Aregbesola.”

Yanzu haka dai saura kwanaki kadan a buga ganganr siyasa a Najeriya, domin samun guraben shugabanci a matakin kasa da jihohi da kuma kananan hukumomin Najeriya a shekarar 2023.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp