Gabanin zaben 2023, gwamnatin tarayya ta shawarci gidajen yada labarai da su guji barin a yi amfani da su wajen bata mutane.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed da Darakta-Janar na Hukumar Yada Labarai ta Kasa, Balarabe Shehu Illela ne suka ba da wannan shawarar a Abuja ranar Talata a babban taron kungiyar yada labaran Najeriya (BON) karo na 76.
Taken taron shine ‘Kawo Al’umma Tare da Sadarwar Zamani a Harkoki Yaɗa Labarai.
Ministan wanda ya samu wakilcin Ayo Adewuyi na Gidan Talabijin na Najeriya, ya bukaci kafafen yada labarai da su bi ka’idojin da suka tanada a cikin kundin tsarin NBC da sauran dokokin da suka hada da sabuwar dokar zabe.
“Ya kamata kafafen yada labarai su taimaka wajen yakar illolin karya ta hanyar yada sahihin bayanai ga jama’a tare da bayar da ra’ayoyin da suka dace daga jama’a ga gwamnati.”
Illela ya nemi kafofin Sadarwar da su daina karfafawa da ba da damar yin amfani da dandamalin su don labarai na karya, ƙiyayya, tsokana da kuma yada jita-jita.