Jigo a jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana yadda ya shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na neman ya gaje shi a 2023, amma bai shirya ya bata masa rai ba.
Ya bayyana haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a lokacin da ya gana da masu fada aji na farko da manyan sarakuna a jihar, a ci gaba da tuntubar juna kan kudirin sa na shugaban kasa a 2023.
Tinubu da mukarrabansa daga Legas sun fara ziyartar Awujale, kuma babban sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona, a Ijebu-Ode.
Daily Trust ta rawaito cewa, Tinubu a takaitacciyar ganawarsa da Awujale ya nemi goyon bayan sarkin kan takararsa ta shugaban kasa.
Ya ce, “Na yi yakin neman zabe domin mayar da Najeriya ga mulkin dimokuradiyya kafin na fara jin ta bakin jama’a cewa, in tsaya takarar shugaban kasa. Na yi tunani sosai game da shi, amma ba zan iya tunaninsa ni kaɗai ba.” A cewar Tinubu.