Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 12 ga watan Yunin 2024 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta bana.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da haka a madadin gwamnati, yana mai taya ‘yan Najeriya murna kan bikin ranar dimokraɗiyya
Tunji-Ojo ya ce, “Yayin da muke sake bikin ranar dimokuradiyya a cikin tarihin kasarmu mai daraja, mu tuna ƙokarin iyayenmu da suka yi kuma mu tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya, amintacciyar kasa da samun zaman lafiya da rashin rabuwan kawuna.”
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da dagewa kan tsarin mulkin dimokradiyya.
Tunji-Ojo ya nanata kudurin shugaban kasa Bola Tinubu na yin gyare-gyare masu kyau don farfado da tattalin arzikin ƙasa da inganta tsaro.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da abokan Najeriya da su yaba da ci gaban da aka samu, tare da fatan samun kyakkyawar makoma ga Dimokradiyyar Najeriya.