Mai ɗakin hamshaƙin ɗan kasuwar nan na jihar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata ta rasu.
Hajiya Rabi Aminu Ɗantata wadda aka fi sani da Mama Rabi ta rasu ne a jiya Asabar a wani asibiti da ke birnin jidda na Saudiyya.
Mama Rabi ta rasu tana da shekaru 70 a duniya, bayan wata doguwar jinya da ta yi fama da ita.
Mama wadda ita ce mace ta biyu (kwari) a gidan fitaccen attajirin, ta mutu ta bar ‘ya’ya shida ciki har da Tajudden Ɗantata, wani ɗan kasuwa mai tashe, da Batulu Dantata da Hafsa Dantata da Jamila Dantata sai kuma Aliya Dantata.
Ta rasu kuma ta bar maigidanta, Alhaji Aminu Ɗantata da jikoki da dama.