Dan wasan Najeriya, Luca Koleosho zai canza sheka daga Espanyol zuwa gasar Premier, Burnley, a bazara, in ji Telegraph.
Koleosho zai koma Turf Moor daga kulob din Spain, Espanyol.
Dan wasan mai shekaru 18 ya riga ya buga manyan wasanni shida a Espanyol.
Burnley za ta biya Yuro miliyan 3 ga dan wasan wanda ya fara buga wa Espanyol wasa na farko da Granada a watan Mayun 2022.
Matashin zai zama kari na shida na Burnley a wannan bazarar.
An haifi Koleosho a Amurka ga mahaifin dan Najeriya da mahaifiyar Italiya-Kanada.