fidelitybank

Ɗan wasan Bayer Leverkusen ya ƙagu ya bugawa Najeriya wasa

Date:

Nathan Tella ya ce “Burinsa zai cika” yayin da yake shirin buga wa Najeriya wasa a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Fifa ta 2026 a mako mai zuwa.

An sanya sunan ɗan wasan, mai shekara 24 da haihuwa, wanda ke wasa a ƙungiyar Bayer Leverkusen, cikin tawagar Super Eagles ta Najeriya da za ta kara da Lesotho da kuma Zimbabwe.

An haife shi a Lambeth, da ke ƙasar Ingila, amma ya cancanci buga wa Najeriya ta dalilin iyayensa, makomarsa ta kasa da kasa ta kasance batu mai mahimmanci tun lokacin da ya fara yin tasiri a ɓangaren matasa a Arsenal.

Tella ya shaida wa BBC cewa, “A kullum batuna wakiltar Najeriya ne.”

“Iyalina za su kasance cikin matukar farin ciki don ganin na cika wannan burin.

“Ina alfahari da asalina na ɗan Birtaniya da Najeriya kuma na yi sa’a da samun al’adu biyu. Tabbas mun haɗa al’adun ɓangarorin biyu, amma gidanmu cikkaken gidan ƴan Najeriya ne ta fannin abinci, da al’adu”

Tella ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan ƙungiyar Burnley a kakar wasan da ta gabata yayin da Clarets suka samu gurbin komawa matakin gasar Firimiya, amma ya koma asalin ƙungiyarsa ta Southampton a ƙarshen kakar wasan.

Ɗan wasan gaban, wanda zai iya taka leda a gefe ko kuma ta tsakiya, ya bayar da gudunmawar ƙwallaye 22 a kakar wasan da ta gabata kuma ya koma Leverkusen a kan farashin fam miliyan 20 a watan Agusta.

Sabuwar ƙungiyarsa ba ta yi rashin nasara ba a gasar Bundesliga na Jamus bayan wasanni 10 kuma ana tunanin bajintarsa za ta ƙara wa tawagar Super Eagles ƙarfi a ɓangaren ‘yan wasan gaba.

Bayan rashin halartar gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022, ‘yan Afirkan ta Yamman sun fara yaƙin neman gurbin shiga gasar ta 2026 inda za su fafata da Lesotho da Zimbabwe a ranakun 16 da 19 ga watan Nuwamba.

Ana sa ran Najeriya za ta tsallake daga rukunin C a saman takwarorinta na Afirka ta Kudu da Benin, inda ƙasashen da suka yi nasara a rukunin za su tabbatar da samun gurbi a gasar da za a yi a ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka bayan da aka ƙara yawan ƙasashe daga 32 zuwa 48.

breaking news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...
X whatsapp