Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka kara a matsayin koma baya na wucin gadi.
A ranar Alhamis ne kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar ta Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.
Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓ a kananan hukumomi uku da suka haɗa da Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Juma’a, gwamna Lawal ya ce an zaɓe shi ne saboda ya tsame jihar daga halin kunci da take ciki.
A cewarsa, sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya nuna abin da mutane suka zaɓa musamma na ganin an samu canji mai kyau da kuma ci gaba.
Ya ce: “Hukuncin da kotun ɗaukaka kara ta yanke, koma baya ne na ɗan lokaci. Duk da haka, ina da kwarin gwiwar cewa abin da mutane suka zaɓa shi za a basu.
Ya yi kira ga al’ummar Zamfara da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce tawagar lauyoyinsa na nazari sosai kan hukuncin domin ɗaukar matakin da ya dace