Dan takarar kujerar Sanatan Jigawa ta tsakiya a jam’iyyar All Progressives Congress APC, Tijjani Ibrahim Kiyawa ya rasu.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa DAILY POST cewa Hon. Kiyawa ya rasu ne a daren jiya da misalin karfe 11:00 na dare a wani asibitin Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Hon. Kiyawa dai fitaccen dan siyasa ne wanda ya taba zama dan majalisar wakilai mai wakiltar Dutse da kuma mazabar Kiyawa ta tarayya daga shekarar 2011-2015 a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya kuma kasance dan takarar gwamna a PDP a zaben 2019 wanda ya sha kaye a zaben fidda gwani a hannun Malam Aminu Ibrahim Ringim.
Kiyawa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC inda ya samu tikitin takarar sanata na jam’iyyar ta Jigawa ta tsakiya a zaben 2023 mai zuwa.
DAILY POST ta ruwaito cewa an yi garkuwa da mahaifiyarsa mai shekaru 75 Hajiya Fatima Ibrahim (Jaja) a kwanan baya a gidanta da ke garin Kiyawa.
Jami’an tsaro ne suka kubutar da ita bayan an gano ta a rukunin gidajen Danladi Nasidi da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Mutuwar Kiyawa na zuwa ne kwanaki kadan bayan rasuwar kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Jigawa Salisu Zakari.


