Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (ACP) Dauda Buba Fika, jami’i ne da ake girmamawa sosai a yakin da Najeriya ke yi da Boko Haram, ya rasu.
Ya rasu ne a babban asibitin kasa dake Abuja da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Talata.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai sharhi kan harkokin tsaro Zagazola Makama ya fitar a ranar Laraba.
ACP Fika ya taka muhimmiyar rawa wajen kwato garuruwa da dama a jihohin Yobe da Borno daga hannun mayakan Boko Haram.
A matsayinsa na Kwamandan Mopol 41, ya jagoranci ayyukan tsaro na hadin gwiwa da suka raunana maboyar ‘yan ta’adda, ciki har da kwato garinsu Fika daga hannun ‘yan ta’adda.
A shekarar 2017, ya samu raunin harbin bindiga a wani samame da aka yi masa a jihar Yobe, raunukan da suka bukaci da a dauki tsawon lokaci ana yi masa magani har sai da ya rasu.