fidelitybank

Ɗan Pantami ya shaƙi iskar ƴanci sa’o’i 24 bayan sace shi

Date:

 

 

 

Ali Isa Ali, ɗan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki ta Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami, ya shaƙi iskar ƴanci, sa’o’i 24 bayan da a ka ce an sace shi.

Jaridar Nation ta rawaito cewa an tsinci Ali, ɗan shekara 14 a wani shingen binciken jami’an tsaro a Ƙaramar Hukumar Dambam, Jihar Bauchi.

An rawaito cewa an yi garkuwa da Ali ne a kan hanyar shi ta dawowa gida bayan an tashe su da ga makarantar islamiyya, inda masu garkuwar da shi su ka yi awon-gaba da shi a kan babur.

Jaridar ta ce babu wani cikakken bayani kan yadda yaron ya kuɓuta, inda ya ke zaune wajen mahaifiyarsa a Bauchi bayan da a ke zargin sun rabu da Pantami.

Nation ta ƙara da cewa mahaifiyar taron ma ta tabbatar da kubutar ta sa, inda ta ce tuni ya na gida tare da ita.

Haka shima Babban Limamin Masallacin Juma’a na Isa Ali, Imam Hussain ya tabbatar da cewa Ali ya kuɓuta kuma ya na wajen mahaifiyarsa.

Jaridar ta ƙarar da cewa da a ka tuntuɓi Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, ya ce bashi da masaniyar sace yaron sabo da ba a kai rahoton ga ƴan sanda ba.

Ya ce ya tuntuɓi caji-ofisoshi cikin garin Bauchi amma duk sun ce basu da masaniya kan lamarin.

daily post news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp