Guda daga cikin masu neman tikitin takarar dan majalisar tarayya daga karamar hukumar Birnin Kano karkashin jam’iyyar NNPP, Yusuf Sharada, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya karbe shi tare da cire masa jar hula.
Wannan dai shi ne karo na farko da guda daga cikin tsagin Kwankwaso ya bar tafiyar tare da komawa tafiyar tsagin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.