Dan majalisar wakilai, Hon. Ekene Abubakar Adams, wanda ya wakilci mazabar Chikun da Kajuru na jihar Kaduna ya rasu.
Ekene, wanda shi ne shugaban kwamitin wasanni na majalisar, ya yi rashin lafiya kuma ya rasu a safiyar ranar Talata, kamar yadda uwargidansa ta bayyana.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan rasuwar wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa, Hon Musliudeen Olaide Akinremi.


