Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa ɗan kirifto mai suna Benjamin Ikaa ɗaurin shekara biyar a gidan yari.
Mai shari’a Emeka Nwite na kotun ne ya yanke masa hukuncin bayan samunsa da laifin damfarar $1.6m.
Benjamin Ikaa ya amsa laifin ɗaya daga cikin laifukan da aka tuhumesa da shi.
Sai dai yana da zaɓin biyan tarar naira miliyan biyar.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta fara kama Ikaa a shekarar da ta gabata kan zargin tafiyar da wani shafin yanar gizo na kirifto, inda yake yi wa mutane alkawarin ninƙa musu kuɗaɗe idan suka zuba jari, abin da ya janyo suka rasa makudan kuɗaɗe.
Benjamin ya miƙa mota ƙirar Toyota Avalon da kuma wayar iPhone 13 ga gwamnatin tarayya.
An kuma gano $11,000 a hannunsa inda za a mayar wa mutanen da ya damfara kuɗin.
Waɗanda ya damfara sun fito ne daga Afrika ta Kudu, Norway, Birtaniya da kuma tsibirin Barbados.