Ɗalibin Jami’ar Usmanu Ɗanfodio, Usman Abubakar Rimi, Dake ajin ƙarshe yana karantar aikin Likita ya rasu a ranar Laraba.
Rahotanni sun ce an yi Jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada garin Mashi, Jihar Katsina.
Idan za’a iya tunawa shine ɗalibin da ya koma sayar da abinci, sakamakon yajin aikin ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.