fidelitybank

Ɗalibin da ya caccaki Aisha Buhari ya ba ta haƙuri

Date:

Aminu Mohammed dalibin shekarar karshe a jami’ar tarayya dake Dutse, ya nemi gafarar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari kan sukar da yayi mata.

Mohammed ya bayyana a shafinsa na twitter a cikin harshen Hausa cewa Aisha ta ci kuɗin talakawa ta yi ƙiba.

Jami’an tsaro ne suka kama shi sannan suka gurfanar da shi a gaban babban kotun tarayya mai lamba 14 na babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai Aisha a ranar Juma’a ta janye karar da ta shigar a kan Aminu Adamu Mohammed.

Lauyan da ke shigar da kara, Fidelis Ogbobe, ya ce janyewar ta biyo bayan tsoma bakin wasu ‘yan Najeriya masu kishin kasa.

Da yake rubuta a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, Mohammed ya ce ba shi da niyyar cutar da ita.

“Zan kuma yi amfani da wannan kafar domin nuna godiya ta ga wadanda suka taimaka min na shiga cikin mafi duhun sa’o’in rayuwata, mutum ba zai iya kubuta daga kaddararsa ba, amma abin da ya faru ya kamata ya zama darasi ga dukkanmu. Na gode duka da ƙauna ɗaya.

“Zan so na yi amfani da wannan kafar domin bayyana bata haƙuri ga wadanda na cutar da su musamman mahaifiyarmu Aisha Buhari. Ba burina bane in cutar da ku kuma insha Allahu zan canza da kyau. Duk da haka, ni ma na gode da gafarar ku, na gode mama.”

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...
X whatsapp