Wasu gungun daliban makarantar sakandire su 10 a jihar Ogun, sun kai wa wani malaminsu hari, wanda ya hana su yin magudi a lokacin jarrabawar zango na uku da ya gabata.
Daliban makarantar Isanbi Comprehensive High School dake Ilisan-Remo a karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun, sun yi zane malamin Kolawole Shonuga a ranar Talata.
An tattaro cewa Shonuga a lokacin da yake zagaya jarabawar gama-gari na daliban aji SS 1, ya kama daya daga cikin yaran mai suna Ashimi Adebanjo mai shekaru 18 yana yin magudi, kuma ya kwace takardarsa.
Wani ganau ya bayyana cewa bayan an kammala karatun sa’o’i ne daliban suka taru a wani wuri, inda suka yi wa malamin duka a kofar makarantar.
An tattaro cewa, daya daga cikin yaran mai suna Kazeem Adelaja ya buga sanda a kan Shonuga yayin da wasu ke dukansa.
A halin da ake ciki, jami’an ‘yan sanda daga reshen Remo sun kama wasu adadi mai yawa na wadanda ake zargin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omotola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, Shonuga ya bayar da rahoton a ofishin ‘yan sanda na Remo, yayin da ya tabbatar da kama mutane 10 da ake zargi.
Shugaban kungiyar malaman makarantun sakandire (ASUSS) na jihar, Felix Agbesanwa ya fusata kan lamarin, inda ya jaddada cewa “duk dalibin da ya daga hannu a kan malaminsa to ya fuskanci fushin doka.”
Shi ma mai baiwa gwamna shawara kan harkokin ilimi, kimiya da fasaha Farfesa Abayomi Arigbabu, ya yi Allah wadai da abin da daliban suka yi tare da shan alwashin cewa, gwamnatin jihar ba za ta amince da ayyukan rashin da’a da dalibai ke yi a fadin jihar ba.